Take a fresh look at your lifestyle.

Sanatan Anambara Ya Raba Kayayyakin Karfafawa Ga Al’umma Sama Da 12,000

97

Dan majalisar da ke wakiltar yankin Anambra ta Arewa a babban zauren majalisa, Sanata Tony Nwoye, ya kammala shirye-shiryen raba kayan karfafawa na miliyoyin naira ga sama da mutane 12,000.

 

An zabo wadanda suka ci gajiyar tallafin ne daga sassa daban-daban na shiyyar majalisar dattawa da kuma fadin jihar.

 

Kayayyakin da dan majalisar ya nuna zai raba sun hada da injin dinki, injin nika, janareta, buhunan shinkafa da kwale-kwale.

 

Da yake jawabi yayin wani taron karfafawa a cocin All Saints Cathedral, wanda aka gudanar da ibadar godiya a cocin All Saints and Holy Trinity Cathedral, Onitsha, Sanatan ya ce ya zaburar da shi wajen bayar da gudummawa ga al’umma.

 

Ya kara da cewa hakan ya yi ne domin cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da nufin inganta rayuwar al’ummar mazabar shi, tare da daukakar Allah kan abin da ya yi ma shi.

 

Yayin da ya ke bayyana cewa taron ba shi da wata manufa ta siyasa, ya yaba wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Mista Peter Obi da Prince Arthur Eze saboda irin gudunmawar da suka bayar a fagen siyasar shi.

 

Dan majalisar ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa al’ummar mazabar shi, inda ya yi nuni da cewa ya jawo wa gwamnatin tarayya tallafin kudi naira biliyan 34 domin aikin hanyar Otucha – Nzam – Ida – Abuja.

Sanatan Anambra ta Arewa Tony Nwoye

 

A nasa jawabin, shugaban jam’iyyar Labour ta jihar, Ugochukwu Emeh, ya lura cewa dan majalisar ya samu nasarori da dama a cikin watanni shida na wakilcin mazabar shi.

 

Ya yi nuni da cewa ‘yan siyasar da aka zaba a karkashin jam’iyyar sun ci gaba da taka rawar gani a fadin kasar nan.

 

Ya yi kira ga masu zabe da su yi aiki domin samun nasarar jam’iyyar a yakin neman mamaye gidan gwamnatin jihar.

 

A nasa gudunmuwar shugaban jam’iyyar Labour Party Caucus na majalisar wakilai, Hon Afam Ogene ya shaida cewar dan majalisar ya nuna hanyar da wasu za su bi domin koyi da haka.

 

Yayin da yake yaba masa kan shirin karfafawa, Hon Ogene ya danganta nasarar da ya samu a siyasance da ikon Allah.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.