Wani hari da ake zargin Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon ya kashe wani babban kwamandan kungiyar Hizbullah ta Radwan a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke balaguro a yankin yana kokarin hana barkewar yakin.
Falasdinawa 249 ne aka kashe tare da jikkata 510 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata a Gaza, in ji ma’aikatar lafiya.
WHO ta ce “ba a san inda majiyyata 600 da ma’aikatan lafiya suke ba daga asibitin shahidan al-Aqsa na Gaza.”
Akalla mutane 23,084 aka kashe da suka hada da yara 9,600 da kuma kusan 59,000 da suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza tun ranar 7 ga Oktoba. Kimanin mutane 1,139 aka kashe a harin farko da Hamas ta kai Isra’ila.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.