Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Anambra Ya Nemi Haɗin Kai Mai Kyau Da Hukumar Kula da Tituna

Usman Lawal Saulawa

0 276

A ci gaban ziyarar aiki da ya kai babban birnin tarayya Abuja, Gwamna Chukwuma Charles Soludo ya ziyarci hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA) a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shugaban hukumar, Engr Nuruddeen Rafindadi.

 

 

Gwamna Soludo wanda ya samu tarba daga Injiniya Rafindadi, ya yabawa hukumar wajen gyaran tituna da kuma kara yin komai ba tare da kudi masu yawa ba.

 

 

Gwamnan ya kuma nemi hadin gwiwa mai inganci’ tare da hukumar kula da gyaran titunan jihar Anambra.

 

 

“Wannan haɗin gwiwa mai albarka da FERMA za a ƙarfafa shi tare da Hukumar Kula da tituna ta Jihar Anambra don tabbatar da hanyoyin da ke cikin Jihar a koyaushe suna cikin yanayi mai kyau. Wannan tsarin hadin gwiwa zai shafi fannonin bayar da kudade, tantance hanyoyin da ke bukatar gyara da kula da yadda za a gyara su da kuma kula da su domin samun saukin zirga-zirga a cikin jihar.”

 

Dangane da shirin hadin gwiwa da jihar Anambra, shugaban FERMA ya yi maraba da wannan ra’ayi, ya kuma ce hukumarsa na fatan yadda za ta yi amfani da wannan hadin gwiwar a nan take da kuma damar da za ta iya kawowa wajen tabbatar da hanyoyin Anambra suna cikin yanayi mai kyau.

 

Idan za’a tuna, a makon da ya gabata ne Gwamna Soludo ya kaddamar da tituna sama da kilomita 80 a jihar Anambra da ke cikin shiyyoyin majalisar dattawa uku.

 

Gwamnan ya kuma yin alkawarin cewa kafin karshen shekara, za a kaddamar da wasu tituna da za su kai kimanin kilomita 220.

 

Ya ba da tabbacin cewa Anambra za ta kasance wata katafaren wurin gine-gine, tare da manyan gine-ginen tituna da sauran ayyukan raya kasa da za’a aiwatar a cikin tafiyar gina kasa ta gari mai rai da wadata a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *