Gwamnatin Somaliya na kokarin kubutar da fasinjojin wani jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya da mayakan Al Shabaab suka kama, amma jami’an soji sun ce zai yi wuya a isa yankin da aka kai su.
Jirgin sama mai saukar ungulu da Majalisar Dinkin Duniya ta kulla yana gudanar da aikin jigilar jinya ta sama lokacin da wata matsala ta fasaha ta tilasta masa yin saukar gaggawa a kusa da kauyen Hind a tsakiyar kasar Somaliya, yankin da mayakan ke iko da shi.
Wasu ‘yan Somaliya biyu da wasu ‘yan kasashen waje da dama na cikin jirgin, kuma da yawa daga cikin ‘yan bindigar sun yi garkuwa da su, in ji jami’an biyu.
Ba a dai bayyana ko nawa aka kama ba da kuma ko akwai wanda ya yi nasarar tserewa.
“Gwamnati na kokarin kubutar da ma’aikatan tun jiya lokacin da hatsarin ya afku, kuma har yanzu ana ci gaba da kokarin,” Ministan yada labarai Daud Aweis ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Bai bada wani bayani ba.
Kanar Abdullahi Isse wanda ke zaune a garin Cadaado mai tazarar kilomita 100 daga arewacin Hindheere, ya ce dakarun da ke yankin ba su da shirin kaddamar da aikin ceto.
“Babu wani soja da ya je ceto su. Ban yi imani za su tsere ba,” inji shi.
“Yankin yana karkashin ikon al Shabaab sama da shekaru goma. Kuma hatta mazauna wurin akwai masu goyon bayan al-Shabaab.”
Manjo Hassan Ali, wanda ke zaune a birnin Beledweyne, inda jirgin mai saukar ungulu ya taso, ya ce ba zai yiwu ba a kai farmaki ta kasa.
“Ban sani ba ko za a samu kwamandojin a cikin jirage tare da taimakon ‘yan kasashen waje. Hakan na iya zama hanya daya tilo da za a iya ceto su, amma har yanzu hakan bai faru ba,” inji shi.
Majalisar Dinkin Duniya ta fada a cikin wani takaitaccen bayani a ranar Laraba cewa ana ci gaba da kokarin mayar da martani.
Ba a samu mai magana da yawun tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Somaliya ba.
Tana da dubban mayaka, mafi yawansu a maboyar ta a tsakiya da kudancin kasar.
Wani harin da gwamnati ta kai tun shekarar 2022 ya yi nasarar kwato wasu yankuna a tsakiyar Somaliya, amma yakin ya fuskanci koma baya a bara.
A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya da ke ba da agajin gaggawa a Somaliya, ta ce jirgin ba nasa ba ne, ko kuma na Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Majalisar Dinkin Duniya, kuma babu wani ma’aikacin da ke cikinsa.
A cikin wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta na X cewa, an dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen na WFP a yankin na wani dan lokaci domin yin taka tsantsan.
Africanews/Ladan Nasidi.