Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Neja Ta Ceto Kaddarori Da Dukiyoyin al’umma

Nura Mohammed, Minna

265

Hukumar kashe gobara ta jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta sami nasarar ceto kaddarori da dukiyoyin al’umma da suka kai kimanin naira miliyan dubu dari biyu a shekara da ta gabata.

 

Shugaban hukumar Baba Alhaji Alkali shine ya bayyana hakan ga manema labarai a ofishin sa dake Minna.

 

Baba Alhaji Alkali ya ce daga farkon janeru zuwa Disamban shekara ta 2023 an sami raguwar tashin gobara da kaso 70 cikin dari, wanda hakan ya sanya hukumar samun nasara a ayyukan ta.

 

Shugaban ya ce a shekarar da ya gabata, hukumar ta gudanar da aikin wayar da kan al’umma a kafefen yada labarai da kuma kasuwanni domin fadakar da jama’a sanin irin hadarin dake tattare da gobara.

 

Ya kara da cewar bisa hakan ne ta sanya aka sami saukin tashin gobarar, lamarin da ya sanya aka sami nasarar ceto kaddarori da dukiyoyin al’umma da suka kai sama da Naira  miliyan dubu biyu a shekarar 2023.

 

“hukumar kashe gobarar  ta kuma sami kiran gaggawa sau 322, yayin da ta sami nasara dakile gobara 345 da ceto rayukan al’umma.”  In ji Shugaban

 

Ya ce an magance matsalolin kararrawar dake nuna alamar tashin gobara da suka sami matsala har 8 da sauran kalubalan da suka shafi gobara a jihar Neja.

 

Baba Alhaji Alkali ya ce mafi yawancin dalilan da suka haddasa gobara a jihar Neja a shekara da ta gabata na da nasaba da wutan lantarki da kuma sakaci daga yara na wasa da ashana.

 

Shugaban ya ce an sami tashin gobara sakamakon wutan lantarki sau 197, an kuma sami gobarar tankin dakon mai  sau 7 a sassan jihar Neja daban daban.

 

Baba Alhaji Alkali ya kara da cewa, “gidaje 215 ne aka sami tashin gobara a cikin su a shekara da ta gabata, yayin da aka sami makarantu 12 da suka sami ifta’lain gobarar duk dai  a shekara ta 2023 .”

 

Ya ce ” Ina shawartar al’umma da su taimaka wa hukumar wajan sanar da ita tashin gobara a dai dai lokacin da abun ya faru, ta yadda zai baiwa hukumar damar kaiwa wurin akan lokaci.”

 

Ya kuma bukaci gwamnatin jihar Neja da ta taimaka wajan kara yawan ma’aikata ga hukumar da kuma samar masu da sabbin Kayayyakin kashe gobara na zamani domin kara inganta ayyukan su.

 

 

Nura Muhammed.

Comments are closed.