Shugaban Kungiyar Zabarkano Ya Bukaci Karin Hadin Kan Mambobin Don Cigaba
By Nura Muhammad, Niger State.
Kungiyar Kabilar Zabarmawa ta Kasa a Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta yaba wa Gwamnatin Jihar bisa irin goyan bayan da suke samu na gudanar da harkokin su a jihar.
Shugaban kungiyar a jihar Neja kana mataimakin Shugaba na kasa na kungiyar ZABARKANO Malam Muktar Muka’il shine ya bayyana hakan a Taron kungiyar na shekara shekara da ya gudana a Minna fadar gwamnatin jihar Neja.
Malam Muktar Muka’il ya kuma yabawa ‘ya’yan kungiyar bisa da’a da kuma biyayya da suke nunawa mahukunta da sauran alumma, wanda hakan ke nuna yadda suke gudanar da harkokin rayuwar su.
Shugaban ya kara da cewar “babban dalilin gudanar da taron a jihar Neja shine domin kara nuna irin soyayya da kuma kaunar juna da aka san Zabarmawa da shi a duk inda aka sami su.”
Shugaban ya kuma godewa wadanda suka halarci taron , musamman sarakunan da suka amsa goran gayyata daga sassan jihar daban daban.
Ana shi jawabin, shugaban kungiyar na kasa Sunusi Yahaya Makera ya godewa gwamnatin jihar da sauran manyan Yan siyasan da ke marawa kungiyar baya na ganin ta sami nasarar tafiyar da harkokin ta.
Ya kuma bukaci ‘ya’yan kungiyar da su kasance jakadu na gari domin kara gyra sunan su a idanun duniya.
A dai taron, Shugabannin kungiyar na jahohi kasan nan da kuma na kananan hukumomin jihar Neja ne suka halarta.