Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da titin Sanata Bola Tinubu a filin jirgin sama na dakon kaya na kasa da kasa na Sam Mbakwe.
Sabon titin da aka kaddamar mai tsawon kilomita 10, Gwamna Hope Uzodinma ne ya gina shi a wa’adin shi na farko daga tituna biyu zuwa hanyoyi hudu tare da fitulun gefen titin Owerri-Aba zuwa filin jirgin sama.
Shugaba Tinubu ya isa filin jirgin saman Dee Sam Mbakwe da ke Owerri da misalin karfe 1:19 na rana agogon kasar a ranar Litinin.
Jamian Tsaro suka gaida Shugaban na Najeriya jim kadan da saukar shi daga cikin jirgi.
Daga cikin wadanda suka tarbi Shugaban har da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, shugaban majalisar, Tajudeen Abbas, mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, shugaban majalisar dattawa. , Godswill Akpabio, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin.
Sauran su ne; Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Alex Otti (Abia), Biodun Oyebanji (Ekiti), AbdulRahman AbdulRazaq (Kwara), Rev. Ft Hyacinth Alia (Benue), Gov Lucky Aiyedatiwa (Ondo), (Kebbi State) Governor, Nasir Idris (Sokoto) Ahmad Sokoto, Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari, Dr Doris Uzoka-Anite, Ministan Kirkira da Fasahar Kimiyya, Uche Nnaji, Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha da Hon. Uche Ekwunife.
Shugaba Tinubu ya samu rakiyar babban sakataren shi, Mista Hakeem Muri-Okunola tare da wasu makusantan shi.
Daga nan ne shugaban ya zarce zuwa filin wasa na Dan Anyiam domin halartar bikin kaddamarwar.