Wata Amalanken jaki dauke da wani abun fashewa da ake zargin bam ne ya tashi a wani shingen binciken ababan hawa da ke kan iyakar Kenya da Somaliya, inda ya kashe dan sandan Kenya daya tare da raunata wasu hudu, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Wani jami’in ‘yan sandan kasar Kenya ya bayar da rahoton cewa, motar ta jawo jakuna guda biyu tare da wani mutum daya ya wuce shingen binciken kasar Somaliya na Bula Hawa, ya shiga cikin kasar Kenya, inda jami’an tsaro suka tare shi domin duba kaya.
Mahayin ya tsallake rijiya da baya, ya koma cikin kasar Somaliya kafin daga bisani ya fashe, lamarin da ya haifar da wata babbar gobara a kan iyakar lardin Mandera da ke arewacin kasar.
Rahoton ya ce ‘yan sandan Somaliya sun kama direban jakin a lokacin da yake kokarin tserewa, kuma rundunar tsaron gundumar Mandera na tattaunawa da ‘yan sandan Bula Hawa domin mika shi ga hukumomin Kenya.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma nan take shakku ya fada kan kungiyar al-Shabab, kungiyar masu tsattsauran ra’ayi da ke Somaliya mai alaka da al-Qaida.
Kungiyar Al-Shabab ta sha alwashin daukar fansa kan Kenya sakamakon tura sojojinta zuwa Somaliya a shekarar 2011 domin yakar mayakan.
Kungiyar ta gudanar da jerin satar mutanen yammacin kasar a cikin Kenya wanda ke barazana ga harkokin yawon bude ido na kasar; babban ginshikin tattalin arzikinta.
Dakarun Kenya sun zama wani bangare na tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka da ta karfafa wa gwamnatin kasar Somaliya mai rauni sama da shekaru 20 a yaki da kungiyar al-Shabab.
Tawagar ta AU a shekarar da ta gabata ta fara janye dakarunta a karkashin wani kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na mayar da iko ga gwamnatin Somaliya.
A cikin ‘yan shekarun nan, hare-haren al-Shabab a Kenya ya takaita ne kawai ga bama-bamai a gefen hanya da aka fi kai wa sojoji da ‘yan sanda.
A ranar Litinin din da ta gabata ne jami’an ‘yan sanda 5 suka samu raunuka bayan da wata motar da suke dauke da su ta tayar da bam a gefen hanya a gundumar Lafey Mandera.
Africanews/Ladan Nasidi.