Take a fresh look at your lifestyle.

Tsohon Shugaban Kasar Saliyo Koroma Zai Yi Jinya A Najeriya

91

Tsohon shugaban kasar Saliyo, Ernest Bai Koroma, zai yi jinya a Najeriya, duk da zargin da ake masa na hannu a yunkurin juyin mulkin bara.

 

Babban Kotun ya ba shi hutun watanni uku, abin da ya jawo cece-kuce game da yiwuwar yin hijira.

 

Mista Bai Koroma, “wanda ya jagoranci Saliyo na tsawon shekaru 11 har zuwa 2018, ya samu izinin barin kasar yayin da yake jiran shari’ar cin amanar kasa da aka shirya yi a watan Maris”.

 

Shugaban kasar na yanzu Julius Maada Bio ne ya gaje shi a ofis.

 

A yammacin ranar Juma’a ne aka hango jirgin shugaban Najeriyar dauke da tsohon shugaban mai shekaru 70 a duniya yana tashi daga filin jirgin saman Freetown.

 

Jita-jita da ake ci gaba da yi na nuni da cewa wata kila kungiyar kasashen yammacin Afirka ta Ecowas tare da hadin gwiwar gwamnatin Saliyo ne suka taimaka wajen bai wa Mista Bai Koroma damar yin kaura, lamarin da zai iya rage zaman dar-dar sakamakon tarzomar da ta barke a watan Nuwamba.

 

Lamarin dai ya biyo bayan rashin tabbas ne, inda masu lura da al’amura ke nuna shakku kan yanayin tafiyar tsohon shugaban da kuma irin tasirinsa ga shari’ar da ke tafe.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.