Najeriya da Indiya sun rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta hadin gwiwa a fannin makamashin da ake sabunta su.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya ce an rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a gefen taron hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Indiya karo na 6, a Abuja.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mista Alkasim Abdulkadir ya sanya wa hannu, Ambasada Tuggar ya bayyana cewa, yarjejeniyar na neman mayar da hankali ne kan bunkasa sabbin fasahohin makamashi da ake sabunta su kamar hasken rana, makamashin iska, Biomass/ Bio-energy, Small Hydro da Capacity Building. .
Ministan ya kuma bayyana cewa taron na kasashen biyu ya shafi bangarori da dama da suka hada da harkokin siyasa, al’adu, sufurin jiragen sama, kasuwanci da zuba jari, hadin gwiwar raya kasa, hadin gwiwar tsaro da harkokin karamin jakadanci da batutuwan shiyya-shiyya da hadin gwiwar bangarori da dama.
A cewar Ambasada Tuggar, Ministan Harkokin Waje na Indiya, Jaishankar, ya kawo ziyara Legas ne inda ya gudanar da tarurrukan da suka dace da dandalin kasuwanci tsakanin Indiya da Najeriya, ya kuma yi jawabi ga Cibiyar Harkokin Kasa da Kasa (NIIA) da ke Legas kan Indiya da Kudancin Duniya. .
Ya ce: “Mun yi shawarwari mai ma’ana sosai a kwamitin hadin gwiwa karo na 6 tsakanin Najeriya da Indiya, an tattauna batutuwa da dama dangane da bangarori daban-daban da suka hada da tattalin arziki, kasuwanci, batutuwan ofishin jakadanci, al’adu da sufurin jiragen sama. Dole ne in ce taron ya kasance mai matukar amfani da wadata. Kun san Najeriya da Indiya suna da kyakawar alaka, mu ne manyan kasashe biyu mafi girma na dimokuradiyya a Nahiyar Afirka da Asiya, mu ne mafi yawan jama’a kuma muna da alaka mai karfi kuma mun kasance abokai na dogon lokaci, dangantakar mu za ta kasance ci gaba da kara karfi,” in ji Ministan.
Ministan Harkokin Waje na Indiya, Jaishankar, ya ce, “Indiya da Najeriya suna da dadaddiyar alakar abokantaka wacce ta samo asali daga tarihi.
“Mu ne mafi girman dimokuradiyya a duniya kuma mu ne shugabanni a nahiyoyinmu. A cikin ‘yan shekarun nan, an sabunta hakan ta hanyar tuntuɓar shugabanninmu,” in ji shi.
Ministan ya kuma bayyana cewa, kasar Indiya na daya daga cikin kasashen da ke kan gaba a fannin tattalin arziki a Najeriya, inda aka kiyasta jarin da aka zuba ya kai dalar Amurka biliyan 27, sannan ana samun karuwar ciniki a duk shekara tsakanin dalar Amurka biliyan 13-15.
Ladan Nasidi.