Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya (FCT), Mista Nyesom Wike, ya warware rikicin da ta dade tana tsakanin kananan hukumomin shida da Kungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya NUT.
Wike ya kuma bayyana cewa an warware takaddamar da ke tsakanin Kansilolin da Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Najeriya (NULGE), daidai wa daida.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron tsaro da majalisar sarakunan babban birnin tarayya Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Idan dai ba a manta ba a ranar 15 ga watan Junairu ne kungiyar NUT reshen babban birnin tarayya Abuja ta umurci malaman firamare a babban birnin tarayya Abuja da su fara yajin aikin sai baba-ta-gani kan rashin biyansu da dama daga cikin hakkokinsu da shugabannin kananan hukumomin yankin suka yi.
Yajin aikin dai ci gaba ne da tun farko da kungiyar ta dakatar a shekarar 2023 kan rashin biyan kashi 40 cikin 100 na Peculiar Allowance da kuma karin karancin albashi na watanni 25 da dai sauransu.
NUT ta dakatar da yajin aikin ne a ranar 2 ga Oktoba, 2023, domin samun damar warware matsalolin cikin makonni shida da ba a cimma ba.
A daya bangaren kuma, NULGE ta yi taho-mu-gama da shuwagabannin kananan hukumomin yankin kan hakkokinsu da suka hada da alawus alawus da kudaden fansho da dai sauran batutuwan da ba a warware ba.
Tun da farko, shugaban majalisar sarakunan babban birnin tarayya Abuja kuma Ona na Abaji, Alhaji Adamu Yunusa, ya yi kira ga ministar da ta shiga cikin rikicin, inda ya koka da yadda yara ke bata lokaci a gida saboda yajin aikin da ake yi.
Da yake sanar da warware takaddamar, ministan ya ce hukumar ta FCTA za ta warware kashi 40 cikin 100 na bashin da ake bin malamai da ma’aikatan kananan hukumomi da ke yajin aiki.
Ya kara da cewa majalisun yankin a bangarensu za su daidaita ragowar kashi 60 cikin 100.
“Na gana da kungiyar NUT da shugabannin kansilolin yankin. To, abin da muka yi; bashin da kananan hukumomi ke da shi, FCTA ta shigo ta karbe kashi 40 cikin 100, yayin da majalisun za su daidaita sauran kashi 60 cikin 100.
“Za a yi hakan duk wata, kuma sun amince.
“Haka ma NULGE, FCTA ta dauki kashi 40 cikin 100, su (majalisun yanki) su biya sauran kashi 60 cikin 100.
“Za mu biya kowane wata kuma nan da watanni uku zuwa hudu masu zuwa, za mu gama daidaita bashin,” in ji ministan.
Da aka tuntubi sakatariyar kungiyar ta NUT, Misis Margaret Jethro, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta kara da cewa Wike ya gana da shugabannin kungiyar a makon jiya.
Ta kara da cewa ministar ta yi alkawarin cewa hukumar babban birnin tarayya Abuja za ta daidaita kashi 40 cikin 100 na sama da Naira biliyan 7 na bashin mafi karancin albashin da majalisun ke bin malaman.
Sai dai ta ce ba a cimma matsaya ba kan bashin da ake bin Peculiar Allowance na sama da Naira biliyan 8 na watanni 12, wanda kuma aka gabatar wa ministar domin sa baki.
Ta kara da cewa shugabannin kungiyar ta NUT za su gana da malaman domin gabatar da tayin sannan su yanke shawarar dakatar da yajin aikin ko a’a.