Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77.
Shugaban wanda ya sauka a safiyar Litinin a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe ya samu tarba a hannun Ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello.
A yayin da yake gabatar da jawabin kasa na kasa a taron, shugaban na Najeriya ya tabbatar wa duniya cewa za a gudanar da sahihin zabe a shekara mai zuwa.
Ya kuma halacci taruka daban-daban da takwarorinsa na kasashen duniya, inda ya ba da tabbacin cewa, kalubalen tsaro da ke fuskantar al’ummar kasar nan ba da jimawa ba za su zama tarihi.
Bugu da kari, ya yi kira ga shugabannin Afirka da su kawar da cin hanci da rashawa.
Leave a Reply