Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Fito Da Tsarin Cin Moriyar Ma’adanan Dake Jihar

Kamilu Lawal,Katsina.

358

 

Gwamnatin jihar Katsina dake arewa maso yammacin Najeriya ta bayyana shirinta na bin matakan da ke da akwai wajen ganowa da hakar ma’adanan kasa da jihar take dasu domin inganta tattalin arzikin ta.

 

Shugaban kamfanin ganowa da hakar ma’adanai na jihar Katsina wato KEMCO, Bello Isah Doro shine ya bayyana hakan a ganawarsa da manema labarai a birnin Katsina.

 

Kamar yadda shugaban kamfanin hakar ma’adanan na jihar Katsina ya bayyana, Allah ya fuwacewa jihar Katsina ma’adanai da dama wadanda bincike ya tabbatar da cewa idan aka inganta hanyoyin hakar su jihar Katsina da Najeriya zasu kara samun hanyoyin kudin shiga da za’a iya amfani dasu wajen ayyukan raya kasa da bunkasar tattalin arziki.

 

Daga cikin ma’adanan da ya bayyana da cewa akwai su da dama a sassan jihar daban daban akwai ma’adanin Zinari da na gilashi da ma’danin yin tayil na kawata gine gine da ma’adanin yin batir da dai sauran ma’adanai wadanda kowace kasa zata iya dogaro da su idan ta inganta samarwa da sarrafasu.

 

Bello Doro ya bayyana cewa domin inganta hanyoyin samar da kudin shiga, gwamnatin jihar ta dora ma kamfanin alhakin tabbatar da sahihancin samuwar duk wani ma’adani tare inganta hanyoyin tono shi domin jihar da kasa baki daya su kara samun kudin shiga da nufin bunkasar tattalin arziki.

 

Yace a halin yanzu kanfanin na KEMCO na akan matakin farko na tabbatarwa tare da tantance yawan wuraren da ake hakar ma’adani a fadin jihar domin cigaba da bin matakan da nufin cimma kudurin da aka sanya a gaba.

 

Shugaban na KEMCO ya kuma ce daga yanzu kanfanin zai tabbatar da cewa duk lokacin da aka cimma wata yarjejeniya ta hakar duk wani ma’adani a jihar za’a tabbatar da cewa al’ummar da ma’adanan suke a yankinsu sun amfana da wani mahimmin kaso na amfanin da ma’adanin ya samar.

 

Yace za’a tabbatar da tsarin ne domin inganta yankunan da rayuwar mazauna wuraren kamar yadda yake kunshe a cikin dokar hakar ma’adanai da ka’ida ta yarda da ita.

 

Bello Doro ya bada tabbacin gwamnatin jihar na bin hanyoyin da suka wajaba wajen inganta harkar hakar ma’adanai da nufin bunkasar tattalin arzikin kasa da inganta rayuwar al’ummar jihar.

 

 

Kamilu Lawal.

Comments are closed.