Take a fresh look at your lifestyle.

UNICEF Za Ta Kawo Karshen Cutar POLIO

Binta Aliyu,Kebbi.

203

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tare da hadin guiwar Gidauniya GAGI dakuma UNICEF sun gina cibiyar agajin gaggawa da kayan aikin magance cutar polio dakuma motocin Hilux uku kyauta ga Jihar Kebbi.

 

Babban Daraktan kula da lafiya a matakin farko ta tarayyar nijeriya, Dakta Muyi Aina shine ya bayyana hakan a yayin bukin bude cibiyar Wanda aka gudanar a Birnin Kebbi.

 

Daraktan,Dakta Muyi Aina, yace Ministan lafiya, farfesa, Muhammad Ali Pate ya fito da tsare tsaren da zasu inganta kiwon lafiya a Nijeriya.

 

A nata Jawabin, babbar Daraktan Asusun UNICEF a Nijeriya, Christiana Munduate tace Nijeriya na daya daga cikin kasashe uku a duniya dake fama da cutar polio, a yayin da jihar kebbi ke daya daga cikin jihohi hudu dake dauke da wannan cutar a halin yanzu.

 

 

Binta Aliyu.

Comments are closed.