Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya mika ta’aziyya ga iyalai da abokan arziki na tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim.
Shugaban ya ce ya samu labarin rasuwar Sanata Abba Ibrahim, yayi bakin ciki matuka.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya sanyawa hannu, shugaba Tinubu ya bayyana marigayi Abba Ibrahim a matsayin ‘aboki na musamman kuma cikakken shugaba wanda ya yiwa al’ummar Yobe hidima da kwazo a lokacin da yake siyasa.
“A matsayin shi na Sanata na tsawon shekaru 12, kwarewar shi ta kasance mai jagoranci a Majalisar Dokoki ta kasa. Al’ummai masu zuwa za su tuna da shi a ko da yaushe ya sanya ci gaba da jin dadin jama’a a kan hidimar shi,” in ji Shugaban.
Yace; “A madadin gwamnatin Najeriya, shugaban ya mika sakon ta’aziyyarsa da ta’aziyya ga iyalai, abokan arziki, da abokan marigayi Sanata da gwamnati da jama’ar jihar Yobe.”
Shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin .
Tsohon gwamnan ya rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yayi doguwar jinya a kasar Saudiyya. Yana da shekaru 75 a duniya.
An zabi Marigayi Ibrahim a matsayin dan majalisar dattawa mai wakiltar Yobe ta gabas a shekarar 2007.
Ya sake tsayawa takara ne a ranar 9 ga Afrilu, 2011, a takarar Sanata mai wakiltar Yobe ta Gabas a jam’iyyar ANPP kuma ya yi nasara.
Ladan Nasidi.