ππͺππ π‘ππ‘ πππ‘π’ π¬π π§ππ¬π π π¨π₯π‘π ππ πππ πππ¦π¨ππ πππππππ‘πππ πππ¬ππ‘ π¦ππ π¨π‘ πππ₯ππ‘ πππ₯π π
Yusuf Bala,Kano.
Gwamnan jihar Kano Arewa maso Yamacin Najeriya, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya taya murna ga Dasuki Galadanchi bayan kara samun girma da yayi zuwa matakin Mataimakin Sifeto Janar na βYansandan Najeriya (DIG), mukamin da rundunar βyansandan na Najeriya ta bashi don wakiltar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
A wasika dauke da sa hannun daraktan yada labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa gwamnan a lokacin da yake taya Sifeto Janar na βyansandan na Najeriya sanya lambar karin girman a kafadar sabon mataimakin sifeton βyansandan a shelkwatar ‘yansandan Najeriya da ke Abuja ya bayyana shi a matsayin dansanda da yayi aiki tukuru ga kasarsa har zuwa wannan lokaci.
Gwamnan cikin alfahari ya bayyana sabon mataimakin sifeton βyansandan Galadanchi a matsayin zakakuri da yayi aiki a matakai daban-daban na aikin dansanda wajen kare rayuka da dukiyoyin alβummar Najeriya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf a madadin gwamnati da alβummar jihar Kano ya mika sakon taya murna ga danasalin jihar ta Kano tare da yi masa adduβar Allah Ya yi riko da hannunsa a duk ayyukan da zai yi.
DIG Dasuki Galandanchi dan aasalin jihar ta Kano ne wanda ya rike kujerar mataimaki na sifeton βyansanda matakin AIG mai kula da shiya ta 12 a jihar Bauchi kafin daga martabatarsa zuwa wannan mataki na DIG da hukumar kula da βyansanda ta kasa ta amince a ranar 24 ga watan Janairu, 2024.
Yusuf Bala.