Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Taya Gwamnan Jihar Kwara Murnar Cika Shekaru 64

106

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya gwamnan jihar Kwara kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya Abdulrahman Abdulrazaq murnar zagayowar ranar haihuwar shi.

 

Shugaban kasa Tinubu na murnar cikar kwararre kuma dan siyasa mai cike da tarihi wanda hawansa ofishin Gwamnan zartaswa mai dimbin tarihi ya kawo sauye-sauye ga tsarin siyasar jihar.

 

A cikin sakon taya murna da mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya sanyawa hannu, shugaba Tinubu ya yabawa gwamnan kan shirye-shirye, ayyuka, da tsare-tsare da gwamnatinsa ta bullo da su domin magance muhimman bukatun ‘yan Kwara.

 

Shugaban ya lura da shirin KwaraLEARN, wanda ke neman karfafawa malamai da sake farfado da ilimin injiniya don ci gaba da ci gaban matasan jihar Kwara nan gaba.

 

Shugaban na Najeriya ya kuma yabawa gwamnan bisa “dabi’a, da’a, da kuma gaskiya, wanda ya ce sun kara masa farin jini a tsakanin jama’a tare da fadada karbuwar ci gaban jihar.”

 

Shugaba Tinubu ya yi wa Gwamna Abdulrazaq fatan Allah ya karo shekaru masu albarka tare da samun koshin lafiya da karfin yi wa al’umma hidima yayin da ya kara sheka

 

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.