Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris ya Sauke shugabanin kananan hukumomi da sakatarorin su,biyo bayan kammala wa’adin mulkin su, na shekara biyu.
Kwamishinan Kananan hukumomi da lamuran masarautu a jihar, Alhaji Abubakar Garba Dutsin Mari shine ya bayya na hakan ga yan- jaridu a fadar Gwamnatin dake Birnin Kebbi.
Kwamishinan Kananan hukumomi da lamuran masarautu, Alhaji Abubakar Garba Dutsin Mari yace akasarin sakatarorin kananan hukumomin ‘yan-siyasa ne, hakan yasa, za’a mika wa, Daraktan kula da ma’aikata mulkin kananan hukumomin.
Kwamishinan, yace Gwamnatin Jihar zata gudanar da zaben kananan hukumomin nan bada jimawa ba.
Binta Aliyu.