Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Ziyara A Kasar Faransa

197

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja babban birnin kasar bayan wata ziyarar sirri ta mako biyu a birnin Paris na kasar Faransa.

 

Jirgin shugaban kasar ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe da misalin karfe 9:00 na yammacin ranar Talata.

Shugaban na Najeriya ya samu tarba daga tawagar manyan jami’an gwamnatin tarayya karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, da sauran shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da kuma ministan harkokin wajen kasar. Babban Birnin Tarayya (FTC) Nyesom Wike

 

Haka kuma a filin jirgin akwai Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani da Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur Heineken Lokpobiri da Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS) Yusuf Magaji Bichi da dai sauransu.

 

Idan dai za a iya tunawa shugaban ya tashi daga Abuja zuwa birnin Paris a ranar 23 ga watan Janairu 2024.

 

Wannan tafiya ta karshe zuwa Faransa ita ce ta uku tun bayan da ya zama shugaban kasa.

 

Na farko ya kasance a watan Yunin bara, makonni uku bayan ya hau kan karagar mulki yayin da na biyu ya kasance a watan Satumbar 2023.

 

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.