Take a fresh look at your lifestyle.

Halin da kasa ke ciki: Kakakin Majalisar Wakilai Abbas Ya Yi kira Da a Kwantar Da Hankula

Abdulkarim Rabiu, Abuja

101

Shugaban Majalisar Wakilai Dr. Tajudeen Abbas, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu domin gwamnati na kokarin inganta rayuwarsu.

Ya yi wannan roko ne yayin wani taron manema labarai na duniya kan halin da kasar ke ciki, a Abuja, babban birnin Najeriya.

Ya lura cewa gwamnati ta damu kuma ta sane da radadin da ’yan Najeriya ke fuskanta,  kuma a shirye take ta kawo sauye-sauye.

 yayin da ake fuskantar matsiba a bin mamaki bane mutane su karaya kana mu shiga cikin takaici. Tasirin kalubalen da na zayyana a sama ya shafi kowane gida, da kowane titi, da zukatan kowane dan Najeriya. Duk da haka, a irin waɗannan lokutan ne ainihin ƙarfinmu na kasa dunkulanla yake bayyana. Juriyarmu da haɗin kai sun sa mun wuce  lokuta masu wuya a baya ba, kuma ba ni da shakka cewa waɗannan halayen za su kara kaimu ga nasara a nan gaba.”

Hon Abbas ya yi nuni da cewa saka hannun jari a halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arzikin duniya da matsalolin kasafin kudi ya tabbatar da aniyar gwamnati na kawo karshen rashin tsaro a Najeriya.

 “Ga wadanda bala’in rashin tsaro ya shafa, ina so ku sani cewa gwamnatin ku na jin kukanku da babbar murya. Muna daukar kwararan matakai don magance musabbabin wannan barazana, inda muke amfani da karfin soji da kuma sulhu don tabbatar da tsaron kasa da dukkan ‘yan Najeriya. Kalubalenyana bukatar hakuri da lokaci don warwarewa, amma ina tabbatar muku cewa muna samun ci gaba.”

 Shugaban majalisar ya ce majalisar na sane da kalubalen tattalin arzikin da al’ummar mazabu ke fuskanta a fadin Najeriya.

“A bangaren tattalin arziki, mu ma mun himmatu wajen dawo da koma bayan tattalin arziki da mayar da kasarmu kan turbar ci gaba mai dorewa.  An tsara manufofin gwamnatin da Tinubu ke jagoranta ne don farfado da tattalin arziki, karfafa zuba jari, da samar da ayyukan yi. Mun fahimci gaggawar lamarin kuma muna aiki tukuru don rage wahalhalun da yawancin ku ke ciki.

 “Batun karancin abinci yana damu na. Wadatar abinci yana da mahimmanci ga tsaron ƙasa. Muna aiwatar da ingantattun dabaru don haɓaka  ayyukan noma, inganta hanyoyin samar da kayayyaki, da tabbatar da cewa abinci mai araha ya isa ga kowa, a duk inda yake zaune.

“Ina rokon ku hakuri yayin da wadannan matakan suka fara aiki. Canjin da muke fatan samu ba zai faru dare ɗaya ba. Yana buƙatar lokaci, ƙoƙari, da goyon bayan kowane ɗan Najeriya. Kowannenmu yana da rawar da zai taka a wannan tafiya ta samar da tsaro da wadataccen abinci. Ko kai manomi ne, ko dan kasuwa, malami, ko ɗalibi, gudunmawarka na da muhimmanci. Tare, za mu iya shawo kan waɗannan ƙalubalen, mu gina kyakkyawar makoma ga ƙasarmu. A matsayina na kakakin majalisar ku, ina cike da buri na sabunta fatan Yan Najeriya,  abin da za mu cimma tare,” in ji Dr. Abbas.

Har ila yau ya yi kira ga duk wani dan Najeriya daga arewa zuwa kudu, daga gabas zuwa yamma da su hada karfi da karfe domin marawa manufofin gwamnati baya.

“Mu yi hakuri, mu hada kai wajen cimma manufa daya ta samar da ingantacciyar kasa, mai karfi, da hadin kan Najeriya. Mun zo nan don yin abin da ba a saba yi ba. Za mu tabbatar da cewa mun kawo tallafi ga rayuwarku, ”  Abbas ya kara da cewa. 

Ya kuma jaddada cewa a matsayinsu na wakilan al’ummar Najeriya, majalisar ba za ta iya  kauda kai ba dangane da halin da mutanen da suka zabe su suka shiga domin kare muradunsu.

 “Kudirinmu ne mu ga cewa ‘yan Najeriya a duk inda suke suna gudanar da rayuwarsu ta yau da kullun cikin kwanciyar hankali da sauki. Muna sane da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a sassan kasar nan. A matsayinmu na zaɓaɓɓun wakilai, muna sane da damuwa da wahalar da kowane iyali da aka azabtar da muggan laifuka da tashin hankali mara amfani. Ku sani cewa za mu yi dukkan mai yiyuwa domin share muku hawaye. Muna goyon bayan duk wani dan Najeriya da abin ya shafa kuma mun kuduri aniyar daukar kwararan matakai na doka don karfafa hukumomin tsaro, tabbatar da adalci, da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’ummominmu.”

Shugaban majalisar ya ce babban taro kan sha’anin tsaro da majalisar wakilai za ta shirya zai magance matsalolin tsaro.

“Yayin da muke yaba wa kokarin jami’an tsaro dangane da kishin kasa da jajircewa, dole ne mu jajirce wajen aiwatar da sauye-sauye a inda ya dace. Wadannan dai na daga cikin batutuwan da taron majalisar dokoki kan harkokin tsaro da za a gudanar a nan gaba. Wannan taro da zai zo nan da makwannimasu zuwa, zai ba mu damar ji kai tsaye daga bakin masu ruwa da tsaki a wannan fanni da kuma samar da matakan da za a bi don sabunta tsarin tsaron mu da kuma inganta yadda ake gudanar da ayyukansa da inganci.”

Shugaban majalisar ya ce baya ga inganta harkokin tsaro ta yadda manoma za su samu kwanciyar hankali su koma gonakinsu, majalisar za ta tallafa wa manufofin shigo da kayayyaki da za su daidaita farashin kayan abinci da kuma samar da isassun kayan abinci a farashi mai rahusa, musamman ga al’ummar mazabarmu da ke zaune a yankunan karkara.

 

Abdulkarim Rabiu

Comments are closed.