Take a fresh look at your lifestyle.

Tuggar Ya Nemi Sulhu Domin Dawo Da Kasashen Da Suka Fita ECOWAS

331

Ministan Harkokin Kasashen Waje, Yusuf Tuggar Yace ya kamata ayi amfani da hanyar diflomasiyya da sulhu domin shawo kan Kasashe Mambobin ECOWAS da suka fita daga Kungiyar a kwanaki baya. 

Ya fadi hakan ne a Taron Shugabannin Majalisar ECOWAS da suka halarta a Babban Birnin Tarayyar Najeriya a ranar Alhamis 8 ga watan fabrairu 2024.

Da yake wa Manema labarai na Muryar Najeriya bayani, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya bayyana cewa Yana jaddada muhimmancin Hadin kai da kuma cewa niyar da wasu Kasashe Mambobin ECOWAS suka yi na fita daga Kungiyar abun takaici ne, Amma duk da haka Za’a cigaba da kokari, idan Allah ya ganar da su zasu dawo matsayin su na Mambobin ECOWAS.

Tuggar ya Kara da cewa “ECOWAS an kafa ta ne domin hukuma ba Don gwamnatocin Kasashe ba, saboda haka muhimmancin ta a Kan al’umma da jama’a ne. Idan aka duba wasu Kasashe irin Ivory Coast zaka ga akwai Yan Mali da Burkina Faso, wanda 30% suna zaune a kasar Ivory Coast.”

“Saboda haka idan aka ce wasu Kasashe sun fita, toh suna son Yan Al’ummar su da suke zaune suna cinikayya da rayuwa a can duk su koma Kasashe su. Kuma idan Za’ayi cinikayya dasu, Sai an biya haraji kuma rayuwar ba dadi zata kara ba Sai Dai wahala, musamman ga Kasashen da suka kudiri wannan niyya”.

“Fatan mu shine Za’ayi amfani da diflomasiyya domin yan’uwan mu ne, Muna kaunar su, zamu shawo kan su domin a cigaba da zama a cikin ECOWAS”, in ji Yusuf Tuggar.

Comments are closed.