Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da ba wa Dr. Malami Shehu Ma’aji Lambar Yabo ta kasa (MFR).
Hakan na kunshe ne a wata takarda da ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Mista George Akume ya sanyawa hannu kuma ya aikewa Dr. Malami.
A wasikar mai lamba: FMSDIGA/NHA/001/93, Ministan ya ce: “Ina farin cikin sanar da kai cewa, Shugaban Tarayyar Najeriya, Mai Girma Muhammadu Buhari, GCFR, ya amince a baka lambar yabo ta kasa ta Karramawa a matsayin MFR (Member of Order of the Federal Republic)”.
A cewar Ministan, za a gudanar da bikin bada lambar yabon ne a cibiyar taron kasa da kasa da ke Abuja a ranar 11 ga watan Oktoba, 2022.
Akume ya Kuma taya Dr Shehu Malami murnar karramawar kasa a matsayin MFR.
AK
Leave a Reply