Take a fresh look at your lifestyle.

Magajin Shugaba Buhari Ne Zai Tabbatar Da Nasararsa – Faleke

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 361

Sakataren kwamitin yakin neman zaben  Tinubu, Hon. James Faleke ya ce za a tabbatar da nasarorin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya samu a cikin shekaru takwas da suka gabata ta hanyar wanda zai gaje shi.

Da yake jawabi a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar dake marawa Bola Ahmed Tinubu baya ta Alliance For Democratic Governance and Emancipation of Nigeria (BADGE) wadda ta kawo gudunmawar kayan yakin neman zabe da suka hada da rigunan T-shirts da huluna, da motoci masu dauke hotuna da dai sauransu, Faleke ya ce idan ba a goyi bayan Tinubu ya lashe zaben shugaban kasa na 2023 ba, duk nasarorin da shugaba Buhari ya samu, mutanen da ba sa ganin kimarsu za su ruguza su.

Hon Falake wanda ya yabawa kungiyar a kokarin da suke yi na ganin Tinubu ya samu nasara, da kuma tabbatar da ya lashe zabe mai zuwa, ya ce BADGE na daya daga cikin kungiyoyin da suka zo Sakatariyar da kayan yakin neman zabensu.

Nasarar kowace gwamnati ana auna ta ne da wanda ya gaje ta, idan ba mu yi aiki tukuru don ganin Tinubu ya gaji Buhari ba, duk nasarar da gwamnatin nan ta samu za ta lalace.

“Idan Tinubu ya yi nasara zai tabbatar da cewa nasarar da shugaba Buhari ya samu ta dore, za a samu ci gaba a nasarorin da Buhari ya samu, mu hada kai domin ganin mun cimma hakan, muna nan a kowane lokaci, kar ku yi nisa da mu a wannan kamfen domin za mu fara a ranar 28 ga Satumba, 2023 tare da addu’o’in mabiya addinai da kuma tattaki zuwa dandalin Unity Fountain da ke Abuja.”

Faleke wanda ya bukaci a saka sunayen mambobin Kungiyar BADGE guda biyar a cikin kwamitin yakin neman zaben Tinubu, ya ce: “A yayin da muke shirye-shirye, a ranar 28 ga Satumba, 2022, muna so mu fara da addu’a, mu mika al’amuran ga Allah, sannan mu yi tattaki zuwa dandalin Unity Fountain domin kira ga hadin kan kasar nan,” inji Faleke.

Babban Daraktan Kungiyar BADGE, wanda kuma tsohon mai taimaka wa shugaban kasa ne, Ibrahim Yusuf Ibrahim, ya ce Tinubu mutum ne nagari da ya kamata a ba shi goyon baya ya gaji shugaba Buhari.

“Ya bunkasa Legas kuma ya daga darajar al’ummarsa, muna mara masa baya don ya ci zaben shugaban kasa a 2023 domin a samar da ayyukan yi a kasar nan.

“Kyakkyawan shugabanci shi ne abin da muke so kuma muna rokon Allah Ya ba Najeriya shugaban da zai kawo zaman lafiya, hadin kai da ci gaba, abin da muka kawo a yau shi ne kawai goyon bayanmu ga Tinubu ya gaji Buhari.” Inji Ibrahim.

Shima da yake jawabi, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar BADGE, Salisu Saminu Jibrin Madachi, ya ce suna son yi wa Tinubu yakin neman zabe a dukkan lungu da sako na kasar nan.

“Mun yi wa Buhari aiki, da Gwamnoni, Sanatoci, Shugabannin Kananan Hukumomi suka samu nasara, daya daga cikin Shugaban Karamar Hukumar shi ne kodinetanmu a Katsina.

“Daga rumfunan zabe zuwa unguwanni, zuwa kananan hukumomi, zuwa Jihohi da tarayya, za mu tabbatar mun Kawo wa Tinubu kuriu, dalilin da ya sa muka kai kayan yakin neman zabe,” in ji Madachi

AK

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *