Yukren ta kaddamar da bincike kan zargin da ake yi wa sojojin Rasha na kashe sojojin Yukren takwas da ba su dauke da makamai bayan da suka karbe iko a birnin Avdiivka.
Hukumar tsaron kasar Ukraine karkashin jagorancin ofishin mai shigar da kara na yankin Donetsk, ta bude wani bincike gabanin shari’a kan zargin kashe fursunonin yaki da ba su dauke da makamai a Avdiivka da kauyen Vesele, in ji wata kafar yada labarai ta gwamnati ta Ukrinform a ranar Litinin.
“A karkashin kulawar tsarin kula da ofishin mai gabatar da kara na yankin Donetsk, an fara gudanar da bincike a gaban shari’a game da keta dokoki da al’adun yaki tare da kisan kai da gangan (Sashe na 2 na Mataki na 438 na Criminal Code na Yukren),” Ukrinform kamar yadda hukumar tsaron ta bayyana haka.
Ukrinform ta ce an raba shaidar kashe-kashen ne a manhajar aika sakonni ta Telegram, ciki har da faifan bidiyo da ke nuna wani sojan Rasha yana harbin wasu sojojin Yukren guda biyu da aka kama a kusa da wajen.
Masko ba ta mayar da martani a bainar jama’a ba game da ikirarin.
Yukren ta sha zargin Rasha da kashe-kashen ba bisa ka’ida ba da kuma wasu laifukan yaki tun bayan da Moscow ta kaddamar da wani gagarumin farmaki kan makwabciyarta a watan Fabrairun 2022. Rasha ta kuma zargi Yukren da aikata laifin keta dokokin kasa da kasa.
A ranar Asabar din da ta gabata ce kasar Rasha ta sanar da cewa ta karbe iko a yankin Avdiivka, bayan janyewar sojojin Yukren da ke zama babbar riba ga Masko tun bayan faduwar Bakhmut a watan Mayun da ya gabata.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yaba da kwace birnin a matsayin “wata muhimmiyar nasara” a yakin da aka kwashe kusan shekaru biyu ana gwabzawa.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.