Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Taron AU

99

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Abuja bayan wata ziyarar aiki ta kwanaki hudu da ya yi a babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa, inda ya halarci zaman taro na 37 na shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU.

 

Shugaba Tinubu, wanda ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, da misalin karfe 3:36 na rana, ya samu tarba daga manyan jami’an gwamnati, karkashin jagorancin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Sanata George Akume.

 

Yayin da yake birnin Adis Ababa, AU ta nada Tinubu, da dai sauran abubuwa, a matsayin gwarzon sa na kula da harkokin kiwon lafiya da hadin gwiwar samar da lafiya ga al’umma.

 

Har ila yau, ya bi sahun sauran shugabannin Afirka da su gabatar da shawarwarin warware kalubalen da kasashen ke fuskanta tare da yin shawarwari kan sake mayar da hankali ga kungiyar ta nahiyar domin samar da ingantacciyar hidima a fannoni daban-daban da suka hada da kiwon lafiya, kasuwanci da tsaro.

 

Ya yi amfani da damar, yayin da yake jawabi ga Majalisar a ranar Asabar, ya sanar da nahiyar cewa, Nijeriya a shirye take ta karbi bakuncin babban bankin Afrika a kasarta, bisa yarjejeniyar da ta kulla a baya a yarjejeniyar Abuja.

 

Sauran jami’an gwamnatin da suka je filin jirgin domin tarbar shugaban a lokacin da ya iso, sun hada da shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila; mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu; gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma; Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Abdullahi Ganduje.

 

Sauran sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun; Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; da sauran Hafsoshin tsaro.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.