An ayyana Sanata Monday Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Edo dake Kudancin Najeriya.
Shugaban kwamitin zaben kuma gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ne ya sanar da sakamakon karshe na atisayen bayan kammala tattara sakamakon zaben kananan hukumomin 18.
Sanata Okpebholo ya samu kuri’u 12,433 inda ya kayar da wasu ‘yan takara 11 da suka fafata a zaben da aka sake gudanarwa bayan fafatawar farko da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ta kasa ta bayyana.
Sanatan na daya daga cikin mutane uku da suka yi nasara a zaben ranar Asabar da ta gabata da aka soke.
Tun da farko dai an maye gurbin Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo da Otu wanda a cewar jam’iyyar APC ba zai samu damar sake tsayawa takara ba.
Ladan Nasidi.