Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
Shugaba Tinubu ya ziyarci iyalan marigayi Akeredolu a Owo, jihar Ondo, kwanaki bayan an binne tsohon gwamnan.
Shugaba Tinubu ya ce za a yi wuya a cike gurbin da gwamnan ya bari, yana mai jaddada cewa “gadonsa za su dawwama har abada.”
“Ya nuna jarumtaka da rashin tsoro, musamman a kokarinsa na neman shugabanci nagari. Ya kasance mai ba da shawara marar tsoro, mai sadaukar da kai ga jin daɗin jama’arsa. Za a rika tunawa da jajircewarsa a koyaushe,” in ji Shugaban.
Tsohon gwamnan ya rasu ne bayan ya yi fama da cutar kansar prostate da kuma cutar sankarar jini a ranar 27 ga Disamba, 2023, yana da shekaru 67 a duniya.
Shugaban na Najeriya ya kuma ziyarci Pa Reuben Fasoranti, shugaban kungiyar Afenifere ta kabilar Yarabawa.
Ladan Nasidi.