Gwamnatin Katsina Ta Shirya Taimakawa Manoman Lokacin Noman Rani Domin Wadatuwar Abinci
Kamilu Lawal,Katsina.
Hukumar noman rani ta jihar Katsina ta kammala shirye-shiryen tara bayanai na manoman dake Noman rani a fadin jihar.
Manajan Daraktan hukumar, Abdulkadir Mamman Nasir wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron hadin gwiwa da manoma a Katsina, ya ce shirin wanda ya yi daidai da dabarun gwamnatin jihar na inganta harkar noma shi ma an yi shi ne domin taimakawa manoman wajen inganta noman su da zai samar da nasara da abinci a jihar.
“Wannan na nufin baiwa gwamnatin jihar damar samun sahihin bayanan manoma da nufin gano karin wuraren da za su taimaka musu domin samun wadatar abinci a jihar,” inji shi.
Manajin Darakta ya yi nuni da cewa, domin cimma burin shirin, tuni ma’aikatan da za su gudanar da wannan atisayen suka samu horon da ake bukata domin tafiyar da bayanan manomi.
“Mun riga munyi haɗin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki kuma mun taru a nan, a yau, domin tattauna hanyoyin da za a iya cimma nasarar wannan aikin da ke zuwa nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Abdulkadir Nasir ya yaba wa Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda bisa goyon bayan da ya baiwa hukumar domin samun nasarar aikin ta.
Ya kuma bayyana irin nasarorin da Gwamnan ya samu na inganta harkar noma a jihar.
Manajan Daraktan ya ce “kokarin ya hada da daukar ma’aikatan da za su taimaka wa manoma da kuma samar da taki da sauran kayan amfanin gona a farashi mai rahusa a jihar”.
Kamilu Lawal.