Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Sin Ta Fadada Samun Visa Zuwa Japan Da Sauransu

374

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a ranar Juma’a cewa, kasar Sin za ta fadada shirye-shiryenta na ba da biza zuwa kasashen Japan, Bulgaria, Romania, Croatia, Montenegro da sauran kasashe, daga ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2024 zuwa ranar 31 ga Disamba, 2025.

 

Har ila yau, za ta tsawaita lokacin zaman ba tare da biza zuwa kwanaki 30 daga kwanaki 15 ga ‘yan kasar daga dukkan kasashe 38 da ke cikin shirinta na ba da biza, kamar yadda gidan talabijin na kasar CCTV ya ruwaito.

 

A baya dai kasar Sin ta ba wa Koriya ta Kudu da wasu kasashen Turai tsarin ba tare da biza ba, don habaka harkokin yawon bude ido da kasuwanci a cikin tabarbarewar tattalin arziki.

 

 

Reuters/Ladan Nasidi.

Comments are closed.