Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Abba kabir Yusuf Ya Koka Kan Kalubale A Harkokin Noma

160

Gwamna Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya koka da rashin samun albarkatun gona da kuma asarar da ake samu bayan noma a jihar, yana mai cewa kalubalen na shafar ci gaban fannin.

 

Gwamna Yusuf ya bayyana karancin samun kasuwa da rashin isassun ayyukan kudi a matsayin abubuwan da ke kawo cikas ga harkar noma a jihar.

 

Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin da ta gabata yayin da yake bayyana bude taron yini biyu na shekara biyu kan aiwatar da hanyoyin sauya tsarin abinci a Najeriya na shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas da aka gudanar a Kano.

 

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar shi, Shehu Wada Sagagi, ya ce jihar na alfahari da kasancewa daya dake kan gaba a cibiyoyin noma a Najeriya, inda noma ya zama tushen tattalin arzikin ta.

 

“Manoman mu suna aiki tukuru domin ganin mun samu isasshen abinci, kuma noma na ci gaba da samar da abinci ga sama da kashi 60 na mutanen mu. Duk da haka, muna da cikakkiyar masaniyar cewa wannan sashe yana fuskantar ƙalubale da yawa, waɗanda suka haɗa da ƙarancin aiki da asarar anfanin gona bayan girbi zuwa kasuwa da rashin isassun hada hadar kuɗi.

 

“Wadannan al’amura ba wai kawai sun shafi bunkasuwar fannin noma ne kadai ba, har ma sun takaita amfanin manoman mu, musamman ma masu karamin karfi. Wannan shine dalilin da ya sa aikin Hanyoyin Sauya Tsarin Abinci na Ƙasa ya dace da lokaci kuma mai mahimmanci”, in ji shi.

 

A cewar shi, aikin ya magance da yawa daga cikin matsalolin da manoman jihar ke fuskanta yayin da ya mayar da hankali kan inganta dabarun noma da suka kunno kai, samun kasuwa, da jure hadurran yanayi zuwa mafi kyawun dabarun shirya abinci.

 

“Hanyoyin Sauya Tsarin Abinci na Kasa yana baiwa manoman mu kayan aikin da suke bukata ba kawai domin tsira ba amma don bunƙasa a cikin yanayi mai ƙalubale”, a cewar Yusuf.

 

Tun da farko, Ko’odinetar shirin a yankin Arewa maso Yamma, Hajiya Lauratu Ado Diso, ta ce shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas sun lalace sakamakon hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan tada kayar baya, lamarin da ya sa ayyukan noma kusan ba zai yiwu ba a wasu yankunan.

 

“Saboda haka, wadannan yankuna sun zama mafi rauni ga kowa, ta fuskar rashin abinci mai gina jiki da kuma yawan yunwa.

 

“Saboda haka, dole ne mu rubanya kokarinmu wajen kawar da wannan matsalar. Dole ne mu sanya dukkan hannayen mu domin yin duk abin da ake bukata don canza wannan mummunan yanayi zuwa mai kyau.

 

“Hakan zai yiwu ne kawai ta hanyar aiwatar da hanyoyin sauya tsarin abinci mai inganci a dukkanin gonaki, kuma zai yiwu ne ta hanyar hadin gwiwa da hadin kai”, Diso, ita ce babbar sakataren ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Kano, in ji ta.

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.