Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar NEMA Ta Fara Kashi Na Biyu Na Tantance Bala’o’i

177

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta fara aikin tantancewar kashi na biyu bayan bala’o’i a jihohi 16 na kasar nan, da nufin tattara bayanai daga al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa a shekarar 2024.

 

Darakta Janar na Hukumar, Mrs Zubaida Umar wacce ta bayyana hakan a Abuja, babban birnin Najeriya, ta ce za a gudanar da tantancewar ne a wuraren da ba a fara aiki da su ba a matakin farko tare da hadin gwiwar hukumomin bayar da agajin gaggawa na jihohi, kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya.

 

Ta bayyana cewa, tantancewar na hadin gwiwa na da nufin samar da sahihin wakilci na gaskiya da rikon amana a fadin jihohin da abin ya shafa.

 

Kashi na biyu na tantancewar zai shafi Abia, Akwa Ibom, Bauchi, Borno, Ekiti, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Lagos, Ondo, Plateau, Sokoto, Yobe, Zamfara, da kuma babban birnin tarayya Abuja.

 

Idan dai ba a manta ba, NEMA ta kafa Cibiyar Ba da Agajin Gaggawa don mayar da hankali kan tattara bayanai dazasu magance bala’in ambaliyar ruwa na 2024.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.