Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Tinubu Ya Maye Gurbin Shugaban Hukumar SEDC Na Farko

154

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya soke sunayen mutanen da aka nada a hukumar raya Kudu Maso Gabas (SEDC), inda ya maye gurbin shugaban farko Emeka Atuma da Dr Emeka Nworgu a matsayin shugaban hukumar na farko.

 

Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar ta bayyana cewa, shugaban ya kuma maye gurbin dukkan manyan daraktocin guda uku da aka nada da farko tare da nada wasu karin daraktoci guda biyu.

 

Onanuga ya kara da cewa shugaban ya kuma cire daya daga cikin mambobin hukumar Donatus Eyinnah Nwankpa.

 

Ya kara da cewa Mark Okoye ya ci gaba da rike mukamin shi a matsayin Manajan Darakta/Babban Jami’in Hukumar a cikin mambobi 16, mamba daya ya fi na farko.

 

Stanley Ohajuruka Sabon babban daraktan kudi shine, wanda ya maye gurbin Anthony Ugbo a jerin farko.

 

Toby Okechukwu shine sabon babban daraktan ayyuka. Ya maye gurbin Obinna Obiekweihe. Cif Sylvester Okonkwo yanzu shine babban daraktan aiyuka na kamfanoni, inda ya maye gurbin Dr Daniel Ikechukwu Ugwuja.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.