Gwamnan Jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya karyata wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na yanar gizo yana zargin wasu ‘yan bindiga sun kori mazauna kauyen Tidibali da ke karamar hukumar Isah daga gidajensu.
Gwamna Aliyu ya yi wannan jawabi ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wajen bikin tunawa da sojojin kasar nan na shekarar 2025 da aka gudanar a Sokoto, inda ya jinjinawa jarumai da suka mutu wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare kasa.
Gwamna Aliyu ya bayyana faifan bidiyon a matsayin karya da yaudara da gangan da wasu mutane da ke jin dadin siyasa da kalubalen tsaro a jihar.
Ya jaddada cewa babu wani lokaci da ‘yan bindiga suka tilastawa mutanen Tidibali gudun hijira.
A cewar Gwamna Aliyu, kwashe mutanen kauyen na wucin gadi wani mataki ne da hukumomin karamar hukumar suka dauka bayan samun sahihin bayanan sirri na cewa ‘yan bindiga na shirin kai wa al’umma hari.
Ya bayyana cewa matakin na kariya ne kawai da nufin kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma bayyana cewa tun daga lokacin an karfafa matakan tsaro a yankin, wanda hakan ya sa aka samu kwanciyar hankali a cikin al’umma.
“Saboda haka mazaunan da aka kora sun koma gidajensu lafiya kuma suna gudanar da harkokinsu na yau da kullun,” in ji shi.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar Jihar Sakkwato cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a duk sassan jihar.
Gwamnan ya yi gargadi game da yada bayanan da ba’a tantance ba yana mai cewa irin wadannan rahotanni na iya haifar da firgici da ba su dace ba da kuma kawo cikas ga kokarin tsaro da ake yi.
Shima da yake jawabi, babban kwamandan runduna ta 8 (GOC) da kuma kwamandan rundunar hadin guiwa ta 2 dake shiyyar arewa maso yamma Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar Ibikunle Ajose, ya ce sojojin na ci gaba da shirye-shiryen ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.
Ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro rahotannin sirri kan lokaci don baiwa sojoji damar daukar matakan da suka dace domin samun dorewar zaman lafiya da tsaro.
A cewarsa, an sadaukar da bukukuwan tunawa da kasa baki daya ne domin girmama jarumtaka, sadaukarwa da kuma jajircewa na jami’an sojan Najeriya wadanda suka biya kudi mai tsoka wajen kare kasar.
Sadaukarwar Jarumta Ya yi nuni da cewa taron ya sake jaddada aniyar kasa baki daya na tunawa da sadaukarwar da jarumai suka yi, ya kuma kara jaddada aniyar rundunar soji na kare zaman lafiya da hadin kai da tsaron Najeriya.
Janar Ajose ya bukaci sojojin da aka tura a ayyuka daban-daban da su ci gaba da jajircewa wajen maido da zaman lafiya da tsaro domin dorewar ci gaban tattalin arzikin kasa.