Take a fresh look at your lifestyle.

Babu Sansanin Sojoji Na Waje A Nijeriya – CDS

135

Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya Janar Christopher Musa ya ce ba za a kafa sansanin soji na kasashen waje a kowane yanki na kasar nan ba.

 

Janar Musa ya bayyana haka ne a wani liyafar cin abincin Kirsimeti na musamman tare da dakarun Operation Fansan Yamma a Barikin soja na Giginya a jihar Sokoto.

 

Ya kuma ba da tabbacin kasashen Nijar da Chadi da Togo da kuma jamhuriyar Benin gwamnatin Najeriya ba za ta kyale wani bakon kasar ya yi amfani da kasarta wajen kai hari kan kasashen da ke makwabtaka da ita.

 

“A Najeriya ba za mu yarda a kafa wani sansani a kasar ba. Muna da kwarewa.

 

“Abin da kawai za mu iya yi shi ne, mu yi atisaye tare, mu je kasashen waje don samun horo su ma su zo Nijeriya, horon musaya kawai muke yi,” inji shi.

 

Ya kuma yi kira ga kasashe makwabta da su yi watsi da duk wata jita-jita da ake yadawa cewa za a kafa wani sansani a Najeriya.

 

“Kwanan nan wasu makwabtan mu sun zargi Najeriya da kyale a yi amfani da kasarta tare da kafa sansaninta na kasashen waje, gwamnatin Najeriya ba za ta taba bari hakan ta faru ba,” in ji shi.

 

Janar Musa ya bukaci kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da Togo da Jamhuriyar Benin da su hada kai da Najeriya domin murkushe ayyukan ta’addanci a yankin.

 

Ya gargadi al’ummomin da ke goyon bayan ayyukan ‘yan ta’addan Lakurawa da su daina irin wannan aika-aika ko kuma su fuskanci illar hakan.

 

“Lakurawa da duk masu tallafa musu su shirya, mun riga mun fara ayyukan mu kuma za mu kara kaimi har sai an fatattake su.

 

“Muna so mu tabbatar da cewa babu wanda zai iya yin garkuwa da duk wani dan Najeriya a duk inda yake a kasar.

 

“Hakkinmu ne da kuma aikinmu mu tabbatar da cewa kowane dan Najeriya ya samu ‘yancin yin aikinsa cikin ‘yanci,” in ji shi.

 

Ya kuma yaba wa sojojin bisa jajircewa da sadaukarwar da suka yi wajen tabbatar da tsaron Najeriya.

 

Ya bukace su da su ci gaba da dagewa da jajircewa wajen sauke nauyin da aka dora musu.

 

“Shekara mai zuwa ta ba mu damar samun gagarumin ci gaba wajen shawo kan kalubalen da ke fuskantar al’ummarmu.

 

“Dole ne mu himmatu wajen tabbatar da cewa shekarar 2025 ta cika da nasarori masu kawo sauyi a dukkan aiyyukan da muke gudanarwa, musamman a Operation FANSAN YAMMA.

 

” Bari in tabbatar muku da tallafin da ake bukata don gudanar da ayyukan ku yadda ya kamata. Jin dadin ku, da na iyalan ku, ya kasance babban fifiko, kuma za mu ci gaba da yin aiki tukuru don ganin an biya muku bukatun ku,” inji shi.

 

Janar Musa ya yi nuni da cewa rundunar sojin Najeriya karkashin jagorancin shi za ta ci gaba da gudanar da ayyukan ta na tsawon lokaci da kuma zamanta a duk inda aka tura sojoji a gida da waje.

 

CDS ya nuna jin dadin shi

Shugaban kasa kuma babban kwamandan sojojin kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar soji da kuma kwarin gwiwar da aka bashi na jagorantar manyan sojojin Najeriya maza da mata.

 

Tun da farko, babban hafsan hafsoshin tsaron ya kaddamar da wasu ayyuka da aka aiwatar a wani bangare na gudunmawar sa a makarantar firamare ta Yahaya Abdulkarim Model inda ya halarta.

 

Ya yaba wa mahukuntan makaranta da shugabannin al’umma bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen ganin an kammala aikin a kan lokaci.

 

Ya bukaci makarantar da ta dauki nauyin gudanar da ayyukan, yayin da ya ba da tabbacin kara shiga cikin makarantar.

 

Shima a nashi jawabin babban hafsan runduna ta 8 da kwamandan runduna ta 2 ta Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar Ibikunle Ajose, sun godewa CDS bisa wannan ziyarar duk da cewa ya yi daidai da jadawalin.

 

Ya ce, abincin rana ba dama ce kawai ta bikin Kirsimeti ba, har ma da yin tunani kan sadaukarwar da aka yi tare, da cimma nasara da warwarewa a matsayin kungiya.

 

GOC ya yaba wa sojojin na jajircewa, juriya da kwarewa wajen sauke nauyin da aka dora musu.

 

“Alkawuran da kuka yi na bakin aiki ya taimaka matuka wajen nasarar da aka samu a aikin FANSAN YAMMA, ku jaruman al’ummarmu ne na gaske.

 

Ya kara da cewa “Ina alfahari da jagorantar irin wannan horo da kuma tantance kungiyar.”

 

Abubuwan da suka fi daukar hankali a ziyarar sun hada da gabatar da abubuwan tunawa ga CDS, ziyarar tsohon filin wasan kwallon kwando da sauran su.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.