Take a fresh look at your lifestyle.

VGN Ta Bukaci Gwamnati Ta Rika Basu Tallafi Don Bunkasa Ayyukan Tsaro

Abdulkarim Rabiu, Abuja

94

Kungiyar Yan sa kai ta Nigeria Vigilante Group (VGN) ta bukaci gwamnatin tarrayar Najeriya da ta rika basu wani tallafi domin gudanar da ayyukan su na tabbatar da tsaro a kasar.

Shugaban kungiyar na kasa Nevy Captain Umar Bakori, shi ne ya bayyana hakan ga maneman labarai a harabar majalisar dokoki ranar Talatar nan, yayin da tawagawar kungiyar ta mika raayinta agame da gyaran kundin tsarin mulki da majalisar za ta yi.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan mika raayinsu ga kwamiktin gyaran kundin tsari na majalisar wakilai, Nevy Kyaftin Umar Bakori ya ce tun kafuwar kungiyar sa kai a Najeriya sama da shekaru 30 da suka gabata, gwamnati bata taba ba su wani tallafi ba duk kuwa da aikin da suke yi na sadaukar da rayuwarsu domin kare lafiya da dukiyoyin alummar kasa.

Ya ce kungiyar tana samun tallafi ne kadai daga alummomin da suke bawa gudunmawar tsaro, da wasu gwamnnatocin jihohi kalilan dake kasar kuma baya isar su wajen gudanar da ayyukan su na yau da kullum.

“Muna so gwamnati ta san da zaman yan Sa kai, ta rika basu wani tallafi wanda yawancinsu manoma ne, ko da a gona mutum zai iya samun dan kudi wanda zai sayi taki, da iri ko injin ban ruwa. A cikinmu a kwai manoma, muna da makiyya da masunta da sauran mutane daban daban, kuma in ban da jihohin Kano da Kebbi, da Abia dakuma Ogun babu gwamnatocin jihohin da suke taimakawa Vijilante” In Ji Nebi Kyaftin Bakori

Dangane da batun kafa yansandan jihohi kuwa, ya ce kungiyarsa bata goyan bayan hakan domin ba zai haifar da, da mai ido ba, hasalima sai dai kara tatarbara cin hanci da rashawa, a don haka ya bukaci gwamnati da ta cire batun a cikin gyaran kudin tsarin mulki. Kana ta kara yawan jamian yansanda da sauran jami’an tsaro na tarayya.

Ya ce a shekarun da suka gabata gwamnatin tarayya ta kashe sama da Naira Biliyan 13 domin fara aiwatar da ayyukan yansandan Al’umma domin taimakawa ayyukan yansanda a fadin kasar. Haka kuma wasu jihohin yankin kudu maso yamma sun kafa kungiyar tsaro ta Amotekum. Jihohin Ekiti da Ondo sun kashe sama da Naira Biliyan 3, yayin da a shekarar 2021 yankin kudu maso gabas suka kafa Kungiyar tsaro ta Ebube , acewarsa Allah kadai ya san nawa suka kashe. Kazalika a ‘yan kwanakin nan Gwamnatocin Zamfara da Katsina sun kashe sama da Naira biliyan 27 domin samar da tsaro a wasu yankuna da suke fuskantar barazana.

Rahotanni sun yi nuni da cewa jihohi 8 sun kashe kusan Naira Biliyan 50 akan sha’anin tsaro amma har yanzu kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

“Wannan abun maganar cin hanci da rashawa ne kawai, an basu kudaden aiwatar da shirin, kuma gwamnonin aka ba Naira biliyan 13.3, ina yansandan al’ummar? An gama da wannan batun yanzu kuma ana maganar yansandan jihohi”. In Ji shugaban Kungiyar ta Bijilante.

Ya ce sha’anin tsaron Najeriya na bukatar daukar kwararan matakai na tunkarar kalubale da barazanar da kasa ke fuskanta. Daya daga ciki shi ne irin rawar da Kungiyar Bijilante ke takawa ta hanyar taimakawa wajen yaki da ta’addanci da masu satar mutane domin karbar kudin fansa, a don haka akwai bukatar sanya ayyukansu a cikin dokokin kasa da suke tafiyar da sha’anin tsaron Najeriya amaimakon kafa ‘yan sandan jiha.

Abdulkarim

 

 

Comments are closed.