Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da mai da hankali da hadin kai, yana mai tabbatar wa ‘yan kasar kudurin gwamnatin shi na yin gyare-gyaren da suka dace da za su samar da ci gaba mai dorewa ga ci gaban kasa.
A cikin sakon shi na sabuwar shekara ga ’yan Najeriya da aka mika wa Muryar Najeriya a ranar Laraba, shugaban ya tabbatar da cewa 2025 na baiwa ‘yan kasa fata da yawa, buri, da kuma fatan samun ingantacciyar ranaku.
Shugaba Tinubu ya ce sabuwar shekara za ta kasance shekara ta cika alkawuran da daukacin ‘yan Nijeriya za su cika burin su na gama-gari tare da kusantar da kowa da kowa zuwa ga kyakkyawar makoma mai kyau da kuma Nijeriya .
“Yayin da muka shiga 2025, ina yiwa kowa fatan alheri da sabuwar shekara. Da fatan za ku kasance masu wadata cikin farin ciki, nasara, da lafiya mai kyau.
“Yayin da sabuwar shekara ke fitowa, tana kawo fata da yawa, buri, da kuma fatan samun ingantacciyar ranaku. Da yardar Allah shekarar 2025 za ta kasance shekara ce ta cika alkawari wadda a cikinta za mu cika burin mu na gamayya.
“Duk da cewa shekarar 2024 ta haifar da kalubale da yawa ga ‘yan kasar mu da gidajen mu, ina da yakinin cewa sabuwar shekara za ta haskaka muna rayuwa.
“Muna kan hanya madaidaiciya da zata gina hamshakiyar Najeriya wacce za ta yi aiki ga kowa da kowa. Kada mu manta da wani dan karamin bangare na al’ummar mu da har yanzu suke kallon al’amura ta hanyar siyasa, kabilanci, yanki, da addini,” in ji Shugaban.
Karanta kuma: Bukukuwa: Gwamnatin Najeriya Ta Sake Tabbatar Da Jin Dadin Jama’a
Shugaba Tinubu ya kara tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa sadaukarwar da suka yi a watanni 19 da suka gabata ba ta zama a banza ba kuma za ta yi amfani a watanni masu zuwa.
Bugu da kari, shugaban na Najeriya ya tabbatar da cewa gwamnatin shi na kan turba mai kyau na gina kasa mai girma da za ta yi aiki ga dukkan ‘yan kasa.
“Ga dukkan ‘yan kasa, sadaukarwar da kuka yi ba ta kasance a banza ba cikin watanni 19 da suka gabata. Ina tabbatar muku ba za su kasance a banza ba ko da a watanni masu zuwa. A tare,za mu tsaya mu ci gaba da aikin gina kasa.
“Sabuwar shekara za ta kusantar da mu zuwa ga kyakkyawar makoma da muke fata da kuma Najeriyar da muke fata.” Shugaba Tinubu ya tabbatar.
Ladan Nasidi.