Take a fresh look at your lifestyle.

RASHIN TSARO SHINE YA KARA FARASHIN KAYAN ABINCI – MANOMA

0 510

Wani manomi a jihar Bernuwai , Tarnongo Viralis yace rashin tsaro ya haifar da hauhawar farshin kayayyakin masarufi saboda akasarin manoman nasansanin’yan gudun hijira a arewa (IDPs) .

Viralis yace a karo na farko a tarihin farashin kayan abinci,yanzu buhun Masara ya kaia Naira dubu N30,000 saboda manoma bazasu iya noma ba saboda tsoron ‘yan taadda da masu yin garkuwa da mutane..

“Abunda ya haifar da hauhawar farashin kayan masarufi shine rashin tsaro,kuma akasarin manoman na sansanin ‘yan gudun hijira ne kuma babu manoman da zasu yi noma shi yasa Abinci yayi tsada.

“Tun da aka haifeni ban taba ganin buhun hatsi ya kai naira dubu N30,000, kuma babu dawa da zai isar da mutane kuma buhun waken soya ya haura Naira dubu N40,000, babu takin zamani maganin feshin kwari saboda haka ne manoma ba zasu iya saye ba”, .

Ladan Nasidi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *