Sojojin Faransa sun taimaka wajen kare fararen hula a lokacin yakin basasa a Ivory Coast daga 2002 zuwa 2007.
Kasar Ivory Coast ta sanar da cewa sojojin Faransa za su janye daga kasar da ke yammacin Afirka, lamarin da zai kara rage karfin sojan da tsohuwar mulkin mallaka ke da shi a yankin.
A jawabin da ya yi na karshen shekara, shugaban kasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, ya ce mataki na nuni ne da zamanantar da sojojin kasar.
A gefe guda kuma, Senegal, wacce a watan da ya gabata ta sanar da cewa Faransa za ta rufe sansanonin sojinta a yankin ta, ta tabbatar da cewa za a kammala janyewar a karshen shekarar 2025.
Kasar Cote d’Ivoire dai ita ce kasa mafi girma da ta rage yawan dakarun Faransa a yammacin Afirka.
Akwai sojojin Faransa kusan 600 a kasar da 350 a Senegal.
Shugaba Ouattara ya ce “Mun yanke shawara bisa hadin kai don janye sojojin Faransa daga Ivory Coast.”
Ya kara da cewa, za a mika bataliyar sojan kasa ta Port Bouét da ke karkashin sojojin Faransa ga sojojin Ivory Coast.
Faransa wadda mulkin mallaka a yammacin Afirka ya kawo karshe a shekarun 1960, tuni ta janye sojojinta daga Mali, Burkina Faso da Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a wadannan kasashe da kuma nuna kyama ga Faransa.
Gwamnatin kasar Chadi – babbar abokiyar kawancen kasashen yammacin duniya a yakin da ake yi da masu kaifin kishin Islama a yankin , ba zato ba tsammani ta kawo karshen yerjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da Faransa a watan Nuwamba.
Shugaban kasar Senegal Bassirou Dioumaye Faye ya bayyana cewa: “Na umurci ministan harkokin sojan kasar da ya gabatar da wata sabuwar koyarwa ta hadin gwiwa a fannin tsaro , wanda ya hada da sauran sakamakon da kawo karshen duk wasu sojojin kasashen waje a Senegal daga shekarar 2025.”
An zabi Faye ne a watan Maris bisa alkawarin samar da mulki da kuma kawo karshen dogaro ga kasashen ketare.
Faransa za ta ci gaba da zama a Gabon.
Shugabannin sojojin Nijar da Mali da Burkina Faso sun matsa kusa da Rasha tun bayan korar sojojin Faransa daga kasashen su.
Daga nan sai Rasha ta jibge sojojin haya a yankin Sahel domin taimaka musu wajen yakar ‘yan tada kayar baya.
Alamu na nuna cewa a yanzu Faransa ta samu kasa da sojoji 2000 a Djibouti da Gabon.
Masu sa ido kan harkokin siyasa na ganin cewa, Faransa na kokarin farfado da rugujewar tasirinta na siyasa da na soja a Afirka.
Da alama dai tsohuwar mai rike da madafun iko ta siyasa a yanzu tana shirin wani sabon dabarun soji na rage alakar soji – matakin da zai rage yawan dakarunta na dindindin a nahiyar.
Fiye da shekaru talatin bayan samun ‘yancin kai daga Faransa, Ivory Coast (wanda kuma aka sani da sunan Faransanci, Cote d’Ivoire) an santa da jituwa ta addini da kabilanci, da kuma ingantaccen tattalin arzikin ta.
An yaba wa kasar ta yammacin Afirka a matsayin abin koyi na kwanciyar hankali. Amma wasu ‘yan tawaye dauke da makamai a 2002 ya raba al’ummar gida biyu. Yarjejeniyar zaman lafiya ta sauya tare da sabbin tashe-tashen hankula yayin da kasar sannu a hankali ta karkata hanyarta zuwa warware rikicin siyasa.
Duk da rashin kwanciyar hankali, Ivory Coast ita ce kasa ta farko da ta fi fitar da waken koko a duniya, kuma ‘yan kasar na samun kudin shiga sosai idan aka kwatanta da sauran kasashen yankin.
BBC/Ladan Nasidi.