Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Kasa Tinubu Da Tijjaniyya Sunyi Addu’ar Samun Zaman Lafiya A Najeriya

2,456

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da Sallar Juma’a tare da jiga-jigan ‘yan uwa Musulmi na Tijjaniyya karkashin jagorancin Khalifa Mahiy Sheikh Ibrahim Inyass da suka kai masa ziyara a fadar gwamnati da ke Abuja.

 

Bayan kammala juma’a na raka’a biyu, shugaban ya gudanar da taron addu’a na musamman ga kasar tare da Khalifa Mahiy da kuma ‘yan uwa musulmi.

A wata zantawa da manema labarai na fadar gwamnati bayan kammala sallar shugaban kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Tijjaniyya, Khalifa Sheik Ibrahim Inyass ya ce shugaba Tinubu na da kyakkyawar niyya ga Nijeriya.

 

Hakanan Karanta: VP Shettima Ya Yiwa Ƙoƙarin Hadin Kan Darikar Tijjaniyya

Shugaban Darikar Tijjaniyya ya ci gaba da cewa ya je Najeriya ne domin yi wa kasar addu’a.

 

“Ina godiya da wannan ziyarar. Ina Najeriya domin yi wa kasa addu’a. Kuma na yi addu’a tare da shugaban kasa. Wannan ya nuna kwakkwaran imani kan yadda shugaban ya damu sosai da Najeriya. Wannan yana nuna kyakkyawar fata ga kasar,” Sheik Mahiy ya kara da cewa.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.