Ana gudanar da taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa, Abuja, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagorantar taron.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da shugaban ma’aikatan tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan.
Haka kuma akwai Ministocin Shari’a, Abubakar Malami, Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Isa Pantami, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Zainab Ahmed, babban birnin tarayya, Mohammed Bello da ilimi, Adamu Adamu.
Sauran sun hada da Ministocin Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, Harkokin Jin kai da kyutata rayuwar Jama’a, Sadiya Farouq, da kuma Karamin Ministan Noma, Mustapha Shehuri, Kasafi da Tsare-tsare na Kasa Clement Agba da Muhalli. Udi Odum.
Sauran mambobin majalisar ministocin suna halartar kusan daga ofisoshinsu da ke Abuja.
Ana sa ran taron na ranar Laraba zai duba daftarin kiyasin kasafin kudin shekarar 2023, wanda shugaba Buhari zai gabatar wa majalisar dokokin kasar a ranar Juma’a 7 ga watan Oktoba.
Cikakkun bayanai daga baya……
Leave a Reply