Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Senegal Za Ta Biya Diyya Ga Iyalan Wadanda Suka Yi Zanga-zangar

109

Hukumomin kasar Senegal sun sanar da shirin bayar da tallafin kudi ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a zanga-zangar da ta barke a Senegal tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024.

 

A wani gagarumin yunƙuri na rama iyalan waɗanda abin ya shafa kowane iyali zai karɓi CFA miliyan 10 wanda hukumomi suka bayyana a matsayin matakin farko na gaggawa. Wannan taimakon na da nufin tallafa wa iyalai da ke baƙin ciki waɗanda da yawa daga cikinsu sun bar mata gwauraye da marayu cikin mawuyacin hali.

 

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil adama na kira da a gudanar da cikakken tsarin shari’a tare da soke dokar yin afuwa mai cike da cece-kuce wadda a halin yanzu ta ke ba da kariya ga wadanda ke da alhakin mutuwar mutane daga fuskantar tuhuma.

 

A halin da ake ciki dai iyalan da suka shigar da kararrakin kisan gilla suna jiran a ba su damar gabatar da kararrakinsu a kotu.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.