Majalisar Dinkin Duniya ta cimma matsaya mai mahimmanci na kaddamar da bincike a hukumance kan take hakkin bil adama da ke faruwa a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
A ranar Juma’a kasashe 47 mambobi na kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya sun kafa wata tawagar bincike cikin gaggawa kan munanan take hakkokin bil’adama da cin zarafi da keta dokokin jin kai na kasa da kasa da aka yi a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
Wannan yanki dai ya yi matukar tasiri sakamakon hare-haren da kungiyar M23 ke ci gaba da kai wa wanda ake zargi da aikata ta’asa da dama da suka hada da kashe-kashe cin zarafin mata da kuma raba dubban fararen hula.
Shugaban Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ya tabbatar da amincewa da kudurin yana mai jaddada cewa wannan mataki na wakiltar wani muhimmin mataki na magance matsalar jin kai da ake fama da ita a yankin.
Binciken dai na da nufin bankado yadda tashe-tashen hankulan suka yi yawa tare da hukunta wadanda suka aikata laifin tare da fatan samar da adalci da zaman lafiya ga al’ummar da abin ya shafa.
Africanews/Ladan Nasidi.