Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu ta yabawa jihar Anambra bisa gaggarumar aiwatar da shirin tallafawa aikin gona na Renewed Hope da aka kammala kwanan nan inda ta bayyana shi ‘a matsayin abin koyi na cimma muhimman manufofin shirin.
Ta ba da wannan yabon ne a yayin taron babban mataki na rubu’i na daya da matan gwamnonin jihohin kasar nan 36 inda ta yaba da dabarun da kuma tsari na Anambra wajen kara tasirin shirin.
A yayin ganawar, Sanata Tinubu ya gabatar da wani faifan bidiyo da ya nuna muhimman lokutan shirin a Anambra.
Ta kuma jaddada gagarumin ci gaban da za a iya samu idan kowace jiha ta yi amfani da irin wadannan dabaru kamar yadda uwargidan Gwamnan, Misis Nonye Soludo ta nuna.
Uwargidan shugaban kasar ta bayyana cewa “kowane bangare na shirin an tsara shi da tunani. Shirin ya fara ne da taron horarwa da aka yi tsawon kwanaki biyu a Polytechnic ta Anambra, Mgbakwu, daga ranar 20 ga Fabrairu zuwa 21 ga Fabrairu 2025 sannan taron karfafawa a dakin taro na Gwamna da ke Amawbia a ranar 26 ga Fabrairu, 2025.”
Misis Tinubu ta yaba musamman yadda Misis Soludo ta jajirce wajen shirin, wanda ya tabbatar da cewa kowane mahalarta ya bar kayan aiki da basira.
Ta ce “Ta wannan yunƙuri jihar Anambra ta kafa tarihi wanda zai iya zaburar da sauran jihohi don yin irin waɗannan tsare-tsare tare da tallafa wa manyan manufofin ci gaban aikin gona a faɗin Najeriya.”
A cewar Misis Nonye Soludo “shekaru daban-daban jinsi da kuma yanayin zamantakewa da siyasa sun shiga cikin shirin ƙarfafawa.Sama da masu cin gajiyar ɗari biyu waɗanda aka zaɓa a hankali don nuna ƙungiyoyin
Sun sami horo na musamman kan sarrafa abincin kaji, noman kayan lambu shigar da ruwa mai ɗigo da kuma kiwon alade tare da ba su kayan aikin da suka dace don ƙaddamarwa da ci gaba da ayyukansu.
Shirin Tallafin Aikin Noma na Renewed Hope wani shiri ne karkashin jagorancin uwargidan shugaban Najeriya Sanata Oluremi Tinubu. Yana daga cikin babban shirinta na Renewed Hope Initiative (RHI) kuma yana da niyyar karfafa manoma inganta samar da abinci, da tallafawa ci gaban tattalin arziki a fadin kasar.
Shirin ya samar da albarkatun noma horo da tallafin kudi ga manoma tare da mai da hankali kan mata matasada gidaje don karfafa noma mai dorewa da dogaro da kai.
Ladan Nasidi.