Take a fresh look at your lifestyle.

DRC Ta Ba Da Ladan Dala Miliyan 5 Ga Shugabannin ‘Yan Tawayen M23

68

Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta sanar da bayar da tukuicin dala miliyan 5 ga kama wasu manyan jagororin ‘yan tawayen M23 guda uku wato tsohon shugaban zaben Corneille Nangaa da kwamandan soji Sultani Makenga da kuma shugaban siyasa Bertrand Bisimwa. An yanke wa mutanen uku hukuncin kisa ne ba sa nan a shekarar da ta gabata saboda cin amanar kasa.

 

Sai dai har yanzu ba a yi yuwuwar kame su ba ganin yadda ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda ke ci gaba da mamaye gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo inda suka kwace manyan biranen kasar kamar Goma da Bukavu. Rikicin da ake ci gaba da yi ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da raba dubban daruruwan fararen hula da muhallansu.

 

Shugaba Félix Tshisekedi ya yi kira da a kakabawa kasar Ruwanda takunkumi na kasa da kasa inda ya bayar da misali da wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da kasancewar sojojin Rwanda 4,000 da ke yaki tare da ‘yan tawayen M23. Gwamnatin Kongo ta kuma bukaci Amurka da ta samar da ma’adanai kai tsaye daga DR Congo maimakon Rwanda wadda ta zarge ta da safarar zinari da coltan ma’adanai masu muhimmanci ga masana’antar lantarki ta duniya.

 

Yayin da Rwanda ke musanta wawure dukiyar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo ta amince da goyon bayan kungiyar M23 tare da tabbatar da ayyukanta ta hanyar da’awar matsalar tsaro kan alakar da ke tsakanin DR Congo da FDLR mayakan da ke da alaka da kisan kare dangi na Rwanda a shekarar 1994 – da’awar Kinshasa ta ki amincewa.

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.