Take a fresh look at your lifestyle.

Firayim Ministan Indiya Ya Ziyarci Mauritius Domin Bukukuwan Ranar Kasa Tattaunawar Kasashen Biyu

95

Firayim Ministan Indiya Narendra Modi ya isa Mauritius a ranar Talata don ziyarar kwanaki biyu inda zai kasance babban bako a bikin ranar kasa karo na 57 na tsibirin a ranar Laraba.

 

A filin jirgin saman Firayim Ministan Mauritius Navinchandra Ramgoolam ya tarbe shi wanda ya koma ofis a karo na uku a 2024.

 

A yayin ziyarar tasa Modi zai gudanar da manyan tarurruka tare da shugabannin kasar tare da mai da hankali kan karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da hadin gwiwar manyan tsare-tsare da hadin gwiwar tsaro da ci gaba a yankin tekun Indiya.

 

Gabanin tattaunawar Modi ya jinjinawa tsohon firaministan kasar Mauritius Seewoosagur Ramgoolam ta hanyar ajiye furanni a wurin tunawa da shi da ke lambun shukar.

 

Ziyarar tasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana goyon bayansa ga yuwuwar yarjejeniya tsakanin Mauritius da Birtaniyya dangane da makomar sansanin sojin hadin gwiwa na Amurka da Birtaniya a tsibirin Chagos.

 

Indiya ta dade tana goyon bayan ikirarin ikon Mauritius akan tsibiran tekun Indiya.

 

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

Comments are closed.