Take a fresh look at your lifestyle.

An Tuhumi Madugun ‘Yan Adawar Tanzania Tundu Lissu Da Cin Amanar Kasa

22

An tuhumi madugun ‘yan adawar Tanzaniya Tundu Lissu da laifin cin amanar kasa kwana guda bayan kama shi bayan wani gangami a yankin kudancin kasar.

 

Wannan tuhuma dai na da nasaba da yakin neman zabensa da ya gudana a fadin kasar na neman a sake fasalin zabe wanda ya ke jagoranta karkashin taken “Babu Sauyi Babu Zabe.”

 

A watan Oktoba ne dai aka shirya gudanar da babban zaben kasar inda ake kyautata zaton Lissu zai kalubalanci shugaba mai ci Samia Suluhu Hassan.

 

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sandan Tanzaniya sun cafke babban dan adawa

 

Lokacin da Samia ta hau karagar mulki a shekarar 2021 bayan rasuwar magabatanta John Magufuli an yaba mata saboda sauya wasu dabi’unsa na neman mulki. Sai dai tun daga nan ake ta sukar ta bayan an kai wa wasu ‘yan adawa hari da kame da kuma sace su.

 

A cikin jerin jawabai da ya yi a bainar jama’a, Lissu yana cewa babu damar gudanar da zabe cikin ‘yanci cikin watanni shida sai dai idan ba a yi gyara ba.

 

Shugaban jam’iyyar Chadema yana son sauya fasalin hukumar zabe. Ya ce bai kamata a hada da mutanen da Samia ta nada kai tsaye ba.

 

A baya an kama Lissu sau da yawa.

 

A shekarar 2017 a lokacin shugabancin Magufuli ya tsallake rijiya da baya a yunkurin kashe shi inda aka harbe shi har sau 16.

 

Daga nan ya tafi gudun hijira kuma ya dawo a takaice a shekarar 2020 domin ya kara da Magufuli a zaben waccan shekarar. Ya fice ne bayan bayyana sakamakon zaben yana korafin rashin bin ka’ida.

 

Daga nan ya dawo a 2023 bayan sauye-sauyen da Samia ta gabatar don ba da dama ga ‘yan adawa.

 

Da sanyin safiyar Alhamis ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa magoya bayan Chadema yayin da suka hana shugabannin jam’iyyar gudanar da taron manema labarai dangane da kame Lissu.

 

Wasu magoya bayan jam’iyyar sun shaida wa BBC cewa babu abin da zai hana su neman a yi musu gyara a zaben kafin zaben.

 

“Mun yi mamakin yadda ‘yan sanda ke tursasa mu a lokacin da taronmu ya kasance cikin lumana” in ji wani mai goyon bayan.

 

“Mun san cewa jam’iyya mai mulki CCM ce ke da hannu a wannan duka, za mu yi gwagwarmaya don kawo sauyi kafin zabe.”

 

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi Allah wadai da amfani da karfi tare da zargin gwamnati da amfani da cibiyoyin gwamnati wajen toshe masu suka.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.