Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyara Na Kwanaki Biyu A Jihar Katsina

299

A yau Juma’a ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa Katsina domin ziyarar aiki na kwanaki biyu da kuma ganawa da masu ruwa da tsaki da kuma duba yanayin tsaro a jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga ya fitar, ta bayyana cewa shugaban zai kaddamar da cibiyar sarrafa kayayyakin gona ta Katsina da kuma titin mota mai tsawon kilomita 24 wanda gwamna Umar Dikko Radda ya kammala.

Onanuga ya kuma bayyana cewa, shugaba Tinubu zai kuma karrama gayyatar da aka yi masa na halartar daurin auren diyar gwamnan kafin ya koma Abuja.

Karanta Haka nan: Ranar Mayu: Shugaba Tinubu ya jaddada sadaukarwar ma’aikata & #8217; Jindadi

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.