Kwamitin majalisar wakilai kan kararrakin jama’a ya gayyaci gwamnonin jihohin Zamfara da Benue tare da shugabannin majalisunsu da su gurfana a gabansu a ranar Alhamis 8 ga watan Mayu domin bayyana dalilin da ya sa majalisar ba za ta karbe ayyukansu ba.
Wannan dai ya biyo bayan koke ne da wata kungiya mai fafutukar kare hakkin jama’a da aka fi sani da masu kula da dimokuradiyya da bin doka da oda ta rubuta, inda ta bukaci majalisar ta karbe ayyukan majalisun dokokin biyu.
Sammacin mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin Mista. Mike Etaba da kansa ya bayyana cewa, wadanda aka gayyata sun riga sun san gaskiyar lamarin.
Etaba ya ci gaba da cewa, “Namu shine mu tabbatar da cewa ana bin doka da oda a kowani lokaci, jam’iyyu na da damar bayyana al’amuransu karara domin ‘yan Najeriya su san abin da ke faruwa.
Aisha.Yahay, Lagos