Take a fresh look at your lifestyle.

Yan sanda Sun Kai Farmaki Maboyar ‘Yan Ta’adda Sun Kwato Alburusai A Jihar Filato.

139

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta samu gagarumar nasara a yaki da miyagun laifuka inda ta kwato harsashi sama da dari biyar a wani samame da suka kai a wata maboyar ‘yan ta’adda a karamar hukumar Jos ta Arewa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Emmanuel Olugbemiga Adesina ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Jos babban birnin jihar.

A cewar CP Adesina an kai harin ne a daren ranar 4 ga watan Mayu 2025 da misalin karfe 9:40. Na dare.

“Jami’an ‘yan sanda sun kai farmaki wata maboyar ‘yan ta’adda da ake zargi da aikata laifuka da ke kan hanyar Bauchi a Jos ta Arewa inda suka gano wata mota kirar Volkswagen Golf Wagon da aka yi watsi da ita mai lamba JJN 812 AH.

A binciken da aka yi wa motar an gano harsashi 500 na 7.65mm” inji shi. Kwamishinan ‘yan sandan ya danganta binciken da ake yi kan wani lamari na kisan gilla da aka yi a ranar 3 ga Mayu 2025 wanda ya shafi kisan wani da ba a tantance ba.

Ya ce kwato alburusai na da matukar muhimmanci wajen bankado laifin. “Wannan wani babban ci gaba ne a kudurinmu na rage laifuka da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Filato. Wadannan alburusai za su iya haifar da mummunar illa a hannun masu aikata laifuka.” Adesina ya bayyana.

Ya kuma tabbatar wa mazauna garin cewa ana ci gaba da kokarin kamo wadanda suka aikata laifin tare da kwato karin makamai. Ya kuma yi kira ga jama’a da su tallafa wa ‘yan sanda ta hanyar ba da bayani mai amfani da zai taimaka wajen gudanar da bincike.

Ya kara da cewa “Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta ci gaba da yin tsayin daka kan aikinta na tabbatar da doka da oda. Mun himmatu wajen samar da yanayi mai aminci da tsaro ga dukkan mazauna yankin,” in ji shi.

Aisha.Yahaya, Lagos

Comments are closed.