Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban kasar Mauritius Ya Yi Alkawarin Hadin Gwiwa Da Kasar Sin

41

Shugaban kasar Mauritius Dharam Gokhool ya bayyana fatansa na karfafa mu’amala da hadin gwiwa da kasar Sin a fannonin tattalin arziki da kasuwanci, da yawon bude ido da yin amfani da tsare-tsare ciki har da dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka da yarjejeniyar ciniki da ‘yanci Mauritius da Sin.

Gokhool ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar takardar shaidar Huang Shifang sabon jakadan kasar Sin a Mauritius.

Ya kara da cewa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu Mauritius da Sin tana da tushe mai zurfi yana mai jaddada cewa Mauritius na dora muhimmanci sosai kan dangantakarta da kasar Sin kuma tsayin daka kan ka’idar Sin.

Huang ta yi alkawarin cika ayyukanta da aminci da aiwatar da ra’ayin shugabannin kasashen biyu da kara amincewa da juna a fannin siyasa da fadada hadin gwiwa ta hanyar da ta dace a fannoni daban daban da nufin bude wani sabon babi na dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Mauritius.

Xinhua/Aisha.Yahay, Lagos

Comments are closed.